An sace wasu kayan tarihi na Holocaust a Jamus – DW – 10/09/2024
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An sace wasu kayan tarihi na Holocaust a Jamus

October 9, 2024

'Yan sandan Jamus na ci gaba da bincike kan sace wasu duwatsu na alfarma kuma na tarihi da ke dauke da sunayen Yahudawan da aka yiwa kisan kare dangi a lokacin mulkin Nazi a yankin Zeitz da ke kudancin Jamus.

https://p.dw.com/p/4lYqD
Duwatsun alfarma na tarihi da aka sace a Trier na Jamus
Duwatsun alfarma na tarihi da aka sace a Trier na JamusHoto: Andrea Grunau/DW

Lamarin dai ya daure kan 'yan sandan yankin na Zeitz da suke ta tararrabin yadda aka sace duwatsun na alfarma da ke dauke da sunaye da shakarun haihuwa na wasu Yahudawa da sojojin Nazi suka halaka su. Galibin jihohin Jamus na da irin wadannan duwatsun da ake likasu a gefen tituna ko kuma a jikin gidajen mutanen da aka yiwa kisan kare dangi a lokacin yunkurin shafe Yahudawa daga doron kasa a zamanin mulkin 'yan Nazi.

Karin bayani: An karrama masu mu'amalar jinsi a taron ta'asar Holocaust

Magajiyar Garin birnin na Zeitz Kathrin Weber ta ce sace duwatsun na tarihi na da alaka da siyasa, a yankin da jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki ke ci gaba da samun farin jini a Saxony.

karin bayani: Jamus: Jimami kan kama karyar 'yan Nazi

Sace kayan tarihin na zuwa a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron alhinin tunawa da Yahudawan da aka yi wa kisan kiyashi a yankin, da tuni mazauna yankin suka kaddamar da asusun tara kudin sake maye guraben duwatsun na tarihi.