Martani kan sake zaben Kais Saied a Tunisiya – DW – 10/08/2024
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Martani kan sake zaben Kais Saied a Tunisiya

Mahmud Yaya Azare
October 8, 2024

Al'ummar Tunusiya na ci gaba da mai da martini kan sakamakon zaben shugaban kasar wanda shugaba mai ci Kais Saied ya samu gagarumin rinjaye,bayan da ya garkame 'yan adawa da abokan takararsa

https://p.dw.com/p/4lXoO
Shugaban Tunisiya Kais Saied
Shugaban Tunisiya Kais SaiedHoto: Tunisian Presidency/APA Images/ZUMA/picture alliance

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar wacce ke yankin arewacin Afirka ta ce Saied ya samu kashi 90% cikin dari na kuri'un da aka kada, tun a zagayen farko, kwana guda bayan kammala zaben da 'yan adawa suka siffanta da na jeka na yika, a kasar dake zama tushen boren neman sauyi a kasashen Larabawar da suka barke a shekarar 2011.

Jim kadan bayan bayyana shi wanda ya lashe zaben da gagarimin rinjaye, Shugaba Kais Saied, mai shekaru 66 da haihuwa ya fada a cikin wani jawabi a hedkwatar yakin neman zaben sa cewa, "Zai ci gaba da tsarkake kasar daga dukkan masu cin hanci da rashawa da kuma mazambata.”

Zaben Tunisiya na 2024
Zaben Tunisiya na 2024Hoto: Yassine Gaidi/Anadolu/picture alliance

"Rokokinmu na yaki na nan dane kan maharbarsu. Za mu ci gaba da yakin da muka fara na barayin gwamnati da 'yan kasuwar da ke ci da gumin talakawa. Mun sai da rayukanmu don cimma wannan burin. Ba za mu lamunta da tafiya tare da duk wani jami'in gwamnatin da ba zai iya sauke nauyin da aka dora masa ba.”

Wannan jawabin nasa dai ya tayar da hankulan masu sukar shugaban kasar ciki har da Sumayyah Isa malama a bangaren shari'a da ke Jami'ar Tunis.

"Bana ganin alamun Tunisiya za ta kai ga tudun na tsira karkashin mulkin kama karya na Kais Saied, wanda ya kware wajen dora laifin gazawarsa a mulki kan 'yan adawa da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati, wadanda abin mamaki, duk da cewa alkalan da ke musu hukunci alkale ne da ya nada. An wanke kusan galibin wadanda aka daure. Bamu da wani zabin da ya rage mana kan banda ci gaba da kalubalantarsa.”

Zanga zangar 'yan adawa gabanin zaben Tunisiya
Zanga zangar 'yan adawa gabanin zaben TunisiyaHoto: Anis Mili/AP/picture alliance

Shi kuwa Salman Hamush, daya daga cikin jagororin jam'iyyun adawa da suka nemi a kaurace wa zaben, cewa yayi dama tun kafin a gudanar da shi an san sakamakonsa: Tuni dai suma magoya bayan shugaban shugaban wadanda suka yi ta bukukuwan murna suka dinga bayyana kyakkyawar fata ga kasar tasu.

"A yau mun dora Tunisiya kan sahihiyar turba da sake zaben Kais Saied da muka yi. A duk 'yan siyasar da suka gabata, babu wanda ya sanya talakawa gaba kamarsa. Duk da adawa da cin kafar da yake fuskanta daga makiya na ciki da waje,yayi nasarar kyautata da inganta rayuwar talakawa,wanda yake samun makarantin yayansa da magunguna da hidimar asibiti kyauta"