Tasirin 'yan Afirka a wasan Turai – DW – 07/13/2024
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Tasirin 'yan Afirka a wasan Turai

Suleiman Babayo
July 13, 2024

Yayin da ake kara wasan karshe tsakanin Spaniya da Ingila, na neman cin kofin Turai da Jamus take daukan nauyi, inda wani abin da ya fito fili shi ne irin kwazon da ake gani na 'yan wasa masu asali daga nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4iFfs
Euro 2024 | Wasan kusa da na karshe | Spaniya da Faransa | Lamine Yamal
Lamine Yamal lokacin wasan Spaniya da FaransaHoto: Manuel Blondeau/AOP.Press/IMAGO

Wannan wasan neman cin kofin kasashen Turai ya dauki hankali masoya kwallon kafa a duniya, kuma duk kasar da ta yi nasarar tsakanin Spaniya da Ingila akwai abu guda da ya fito fili shi ne irin rawar da 'yan wasa masu asali daga nahiyar Afirka suka taka a wannan gasa irin Lamine Yamal da Nico Williams da suke wasa da tawogar Spaniya gami da Bukayo Saka mai wasa da tawogar Ingila. Shi dai Nico Willams an haifeshi a Spaniya yayin da iyayensa suka fito daga Ghana, shi da yayansa, Inaki suna wasa da kungiyar Athletic Bilbao a wasannin lig na La Liga na Spaniya. Shi dai Inaki ya zabi wasa da kasar Ghana, ya nuna kansa lokacin wasan neman cin kofin duniya na shekara ta 2022.

Karin Bayani: Aski ya zo gaban goshi a gasar Euro 2024

Lionel Messi da Lamine Yamal
Lionel Messi yana wanka wa Lamine Yamal lokacin Yamal yana karamiHoto: Joan Monfort/AP Photo/picture alliance

Shi kuma Lamine Yamal wanda ya cika shekaru 17 a wannan Asabar, iyayensa sun fito daga kasashen Equatorial Guinea da Moroko. Yamal ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya jefa kwallo a raga a wasannin neman cin kofin kasashen Turai, yana da shekaru 16 gabanin ya cika 17.

Hotunan da Lionel Messi shahararren dan wasan Ajentina da ke yi wa Lamine Yamal wanka a shekara ta 2007, sun karade kafofin Intanet, saboda kwazon da Yamal yake nunawa a wasannin kasashen Turai, a wannan lokaci kuma  Lionel Messi ya jagoranci kasarsa ta Ajentina zuwa wasan karshen na neman cin kofin kasahsen yankin Amirka na Copa.

Euro 2024 wasa tsakanin Denmak da Ingila
Bukayo Saka lokacin wasan Ingila da DenmakHoto: Thanassis Stavrakis/AP/picture alliance

Ita ma Ingila da ta kai wasan karshen tana da shaharraun 'yan wasa masu asli daga Afirka kuma Bukayo Saka na daga ciki. Iyayen Saka fito ne daga Najeriya. Dan wasan kungiyar Arsenal duk ya ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshen shekara ta 2021, amma yanzu yana cikin 'yan wasan da suka taimaki Ingila zuwa wasan karshe. Jacob Mulee, tsohon mai horas da 'yan wasan Kenya wanda yake ganin akwai abin da suke karawa wasa, idan aka cire sai wasan ya zama babu karkashi.

Euro 2024 | Wasan kusa da na karshe | Spaniya da Faransa | Marc Cucurella
Spaniya bayan samun nasaraHoto: Michaela Stache/REUTERS

Wannan wasan neman cin kofin kasashen Turai na zuwa lokacin a bangaren siyasa masu matsanancin ra'ayin kin jinin baki suke kara tasiri, da neman tsauraran manufofin shige da fice.